@nasiram
Hukumomin tsaro a jihar Kano sun sanar da dakatar yin amfani da Babur (Machine) wajen daukan mutane ko sana'ar Achaba (dama tun sama da shekaru 10 an dakatar).
Haka kuma an dakatar da yin amfani da zirga zirgan Keke Napep daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safiyar kowace rana daga yanzu (har sai abubuwan dai daita kuma gwamnatin ta sake yin sanarwa).
Wannan dokar ta shafi Kananan hukumomi kamar haka:
1. KMC
2. Gwale
3. Dala
4. Fagge
5. Nasarawa
6. Tarauni
7. Kumbotso
8. Ungogo (Jido).
9. Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya, da Jido).
Haka kuma duk wanda yaga wani abunda ya kamata a sanar da jami'an tsaro ya sanar ta hanyar kiran wadannan layi:
08032419754
08123821575
09029292926
Muna fatan mutane suyi hakuri da 'dan matsin da za'a shiga, kuma a bayar da hadin kai wa jami'an tsaro wajen yin aikin tabbatar da zaman lafiya.
Allah ya tsare jihar Kano, Arewa da Nigeriya gaba daya.