nasriliumjagaban pfp
nasriliumjagaban

@nasriliumjagaban

Yadda Wani Dreban Trela Ya K@she Miji, Mata Da Ɗansu A Daren Jiya, A Kagoro By Express Kuma Ya Gudu😢! Dreban trela ya niƙe mutum uku a daren jiya, ƙafafuwansu ne kaɗai suka rage a ƙoƙarinsu na tsallakawa, wannan bashi bane karo na farko, daga fara aikin wannan hanya zuwa yanzu ansamu asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske, banda ɗan banzan go slow dake haɗuwa a hanyar dare da rana. Tun daga jajare har unguwar mu'azu wuri biyu nè kawai aka abuɗe inda mutane suke iya samu su tsallaka😢. Wannan hanya ta zamewa masu shige da fice tsakanin igabi da kaduna south tamkar maƙabarta, duk wanda zai tsallaka ko zai tsallako cikin fargaba da ɗar-ɗar yake saboda tsoron abinda zaije ya dawo. Don Allah gwamnatin jihar kaduna ƙarƙashin jagorancin gwamna Uba Sani ayi wani'abu akan wannan hanya.
0 reply
0 recast
0 reaction